Wednesday, 29 June 2016

TARIHIN T.Y BURATAI.

TARIHIN TUKUR YUSUF BURUTAI. . Lieutenant General Yusif Tukur Buratai: . Sunansa Tukur Yusuf Buratai, amma ana kiransa da ‘T.Y Buratai’. An haife shi a garin Buratai dake karamar hukumar Biu ta jihar Borno, a ranar 24 ga watan Nuwamba a shekarar 1960. Don haka, Buratai ɗan asalin jihar Borno ne dake arewa maso gabashin Najeriya. ↓ Laftana Janar TY Buratai shi ne hafsan Sojoji na 26 a tarayyar Najeriya, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya naɗa a ranar 13 ga watan Juni na shekarar 2015. ↓ Buratai ya yi karatun Furamari a garinsu buratai, daga nan ya zarce zuwa Kwalejin Malaman Gwamnati dake garin Potiskum a jihar Yobe. A watan Junairu na shekarar 1981, Buratai ya halarci Nigerian Defence Academy dake Kaduna a matsayin ɗaya daga cikin membobi a shirin nan na ‘29 Regular Combatant Course (29R)’. Haka zalika, Buratai ya samu takardar shaidar kammala Jami’a, wato Digiri a fannin History daga Jami’ar Maiduguri. Kuma yana da Digiri a fannin Philosophy daga Jami’ar Bangladesh University of Professions dake garin Dhaka. ↓ Kafin naɗinsa a matsayin hafsan Soji, Buratai shi ke jagorantar rundunar tsaro ta hadin–gwiwa wacce ke da hedikwata a birnin Ndjamena na kasar Chadi. Kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da kuma Benin ne suka kafa rundunar domin yaki da ’yan ta’addan da ke yankinsu. ↓ A baya dai, Janar Buratai ya yi aiki a matsayin Kwamandan runduna ta Biyu ta sojin Najeriya dake birnin Fatakwal na jihar Rivers, sannan ya taba zama Kwamandan makarantar horas da sojin kasa dake Jaji, a jihar Kaduna. ↓ TY Buratai ya samu ci gaba ainun wajen aikinsa da kuma karin girma kamar haka: • Lieutenant (January 1985) • Captain (January 1989) • Major (January 1994) • Lieutenant Colonel (January 1998) • Colonel (January 2004) • Brigadier General (January 2009) • Major General (January 2012) • Lieutenant General (August 2015) ↓ TY Buratai ya samu kambi da lambobin yabo a wurare daban–daban da suka haɗa da: • Forces Service Star (FSS) • Meritorious Service Star (MSS) • Distinguished Service Star (DSS) • Grand Service Star (GSS). • Pass Staff Course Dagger (PSCD) • Field Command Medal • Training Support Medal • United Nations Medal for Angolan Verification Medal II 26-12-2015 Allah ya karawa rayuwar ka albarka T.Y burutai, ya baka ikon yin daidai, ya kare ka daga dukkan sharri, ya kuma hadaka da dukkan alkhairi. Amin.

2 comments: