Sunday, 12 June 2016
JIHAR BORNO TA SHAFE SAMA DA WATA DAYA BABU WUTAR LANTAR KI.
Al-ummar jihar borno sun shafe sama da wata daya, basu da wutar lantar ki, kuma suna cikin matsanan cin wahala saboda yanayin zafin da suke ciki kuma basa samun ruwan sha mai sanyi, yanda ya kamata, kwamakin baya mai martaba shehun borno Umar Garbai el-amin elkanami, yayi kira da a gaggauta kawo wuta dan al'umma ta samu sa'idar rayuwa, amma har yanzu suna fiskan tar wannan matsala, inda zafin rana yana kai wa digiri 40% na rana, wanda yasa al'umma dewa na jikkata.
Da muka tun tubi wani babban jami'in wutar lantar ki na jaha wanda bai son bayyana sunan sa ba, yace, "Wasu manyan tirasfomomi ne suka lalace akan hanyar Biu zuwa maiduguri, kuma yace, "injinonin su suna kan gyarawa dan haka al'umma suci gaba da hakuri.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment