Wednesday, 29 June 2016
AN SHAFE SAMA DA WATA UKU BABU WUTAR LANTAR KI A BORNO
AN SHAFE WATA UKU BABU HASKEN WUTAR LANTARKI A BORNO.
Daga wakilin mu BIN ISMAIL ALI MAIDUGURI.
Yau kimanin wata uku kenan babu hasken wutar lantarki a jihar borno, wanda haka yasa jama'a cikin kakani kayi inda, wanda har takai mai martaba shehun BORNO kira akan ayi gaggawa a samarwa jahar wutar lantarki, dan su samu susha ruwa mai sanyi a wannan wata mai albarka, amma gashi mun doshi karewan wannan wata na Ramadan amma har yanzu babu alamar wuta a jihar wanda har takai wasu na cewa, "kodai mun sallamo wutar ne baki daya.
Wakilin mu ya zaka dan ganewa idanun sa yanda mutane suke rayuwa tun bayan daukewar wutar lantarki, jama'a dewa sun bayyana cewa, "abun yazo musu ne ba zata inda da wasa -wasa har yanzu mun shafe wata uku. Shi kuma assale MUHAMMAD Tahir cewa yayi, "muna cikin matsanan cin wahala na samun ruwan sha musamman a wannan wata mai albarka, inda ya kara da cewa, "in kaga wuta to sai wanda yake da hali wato yana da injin bada wutar.
Sai dai duk kokarin da wakilin mu yayi na jin ta bakin jami'an wutar lantarki ya ci tura inda ya ziyarci ofishin su bai samu kowa ba.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment