BORNO HAUSA
Wednesday, 29 June 2016
AN SHAFE SAMA DA WATA UKU BABU WUTAR LANTAR KI A BORNO
AN SHAFE WATA UKU BABU HASKEN WUTAR LANTARKI A BORNO.
Daga wakilin mu BIN ISMAIL ALI MAIDUGURI.
Yau kimanin wata uku kenan babu hasken wutar lantarki a jihar borno, wanda haka yasa jama'a cikin kakani kayi inda, wanda har takai mai martaba shehun BORNO kira akan ayi gaggawa a samarwa jahar wutar lantarki, dan su samu susha ruwa mai sanyi a wannan wata mai albarka, amma gashi mun doshi karewan wannan wata na Ramadan amma har yanzu babu alamar wuta a jihar wanda har takai wasu na cewa, "kodai mun sallamo wutar ne baki daya.
Wakilin mu ya zaka dan ganewa idanun sa yanda mutane suke rayuwa tun bayan daukewar wutar lantarki, jama'a dewa sun bayyana cewa, "abun yazo musu ne ba zata inda da wasa -wasa har yanzu mun shafe wata uku. Shi kuma assale MUHAMMAD Tahir cewa yayi, "muna cikin matsanan cin wahala na samun ruwan sha musamman a wannan wata mai albarka, inda ya kara da cewa, "in kaga wuta to sai wanda yake da hali wato yana da injin bada wutar.
Sai dai duk kokarin da wakilin mu yayi na jin ta bakin jami'an wutar lantarki ya ci tura inda ya ziyarci ofishin su bai samu kowa ba.
TARIHIN T.Y BURATAI.
TARIHIN TUKUR YUSUF
BURUTAI.
.
Lieutenant General Yusif Tukur
Buratai:
.
Sunansa Tukur Yusuf Buratai, amma
ana kiransa da ‘T.Y Buratai’. An haife
shi a garin Buratai dake karamar
hukumar Biu ta jihar Borno, a ranar
24 ga watan Nuwamba a shekarar
1960. Don haka,
Buratai ɗan asalin jihar Borno ne
dake arewa
maso gabashin Najeriya.
↓
Laftana Janar TY Buratai shi ne
hafsan Sojoji na
26 a tarayyar Najeriya, wanda
shugaban kasa
Muhammadu Buhari ya naɗa a ranar
13 ga watan
Juni na shekarar 2015.
↓
Buratai ya yi karatun Furamari a
garinsu buratai, daga nan ya zarce
zuwa Kwalejin
Malaman Gwamnati dake garin
Potiskum a jihar Yobe. A watan
Junairu na shekarar 1981, Buratai ya
halarci Nigerian Defence
Academy dake Kaduna a
matsayin ɗaya daga cikin
membobi a shirin nan
na ‘29 Regular Combatant Course
(29R)’. Haka zalika, Buratai ya samu
takardar
shaidar kammala Jami’a, wato Digiri
a fannin History daga Jami’ar
Maiduguri. Kuma yana da Digiri a
fannin Philosophy daga Jami’ar
Bangladesh
University of Professions dake garin
Dhaka.
↓
Kafin naɗinsa a matsayin hafsan Soji,
Buratai shi
ke jagorantar rundunar tsaro ta
hadin–gwiwa
wacce ke da hedikwata a birnin
Ndjamena na kasar Chadi. Kasashen
Najeriya
da Nijar da Kamaru da Chadi da kuma
Benin ne suka kafa rundunar domin
yaki da ’yan ta’addan da ke yankinsu.
↓
A baya dai, Janar Buratai ya yi aiki a
matsayin
Kwamandan runduna ta Biyu ta sojin
Najeriya
dake birnin Fatakwal na jihar Rivers,
sannan ya
taba zama Kwamandan
makarantar horas da
sojin kasa dake Jaji, a jihar
Kaduna.
↓
TY Buratai ya samu ci gaba ainun
wajen aikinsa
da kuma karin girma kamar haka:
• Lieutenant (January 1985)
• Captain (January 1989)
• Major (January 1994)
• Lieutenant Colonel (January 1998)
• Colonel (January 2004)
• Brigadier General (January 2009)
• Major General (January 2012)
• Lieutenant General (August 2015)
↓
TY Buratai ya samu kambi da
lambobin yabo a
wurare daban–daban da suka haɗa
da:
• Forces Service Star (FSS)
• Meritorious Service Star (MSS)
• Distinguished Service Star (DSS)
• Grand Service Star (GSS).
• Pass Staff Course Dagger (PSCD)
• Field Command Medal
• Training Support Medal
• United Nations Medal for Angolan
Verification
Medal II 26-12-2015
Allah ya karawa rayuwar ka albarka
T.Y burutai,
ya baka ikon yin daidai, ya kare ka
daga dukkan
sharri, ya kuma hadaka da dukkan
alkhairi. Amin.
Tuesday, 28 June 2016
KOTU TA BADA UMARNIN GARKAME KAYODE
Kotu Ta Bada Umarnin Garkame Fani
Kayode, Nenadi Usman
Wata kotun tarayya ta bada umarnin
garkame tsohon Ministan Sufurin
jiragen sama, Fani Kayode da
takwararsa na ma'aikatar kudi, Nenadi
Usman bisa zargin almundahanar
Naira Bilyan 1,5.
Mai Shari'a kotun, Suleman Hassan
ya ki bada belinsu ne bayan da
lauyan EFCC ya nemi a bashi lokaci
don yin nazari kan bukatar wadanda
ake tuhumar na neman beli.
Kudaden dai na daga cikin kudaden
makamai wadanda aka yi amfani da
su a lokacin yakin zaben Jonathan
wanda Fani Kayode ne mai Magana
da yawun kungiyar yakin neman
zaben.
Sunday, 12 June 2016
JIHAR BORNO TA SHAFE SAMA DA WATA DAYA BABU WUTAR LANTAR KI.
Al-ummar jihar borno sun shafe sama da wata daya, basu da wutar lantar ki, kuma suna cikin matsanan cin wahala saboda yanayin zafin da suke ciki kuma basa samun ruwan sha mai sanyi, yanda ya kamata, kwamakin baya mai martaba shehun borno Umar Garbai el-amin elkanami, yayi kira da a gaggauta kawo wuta dan al'umma ta samu sa'idar rayuwa, amma har yanzu suna fiskan tar wannan matsala, inda zafin rana yana kai wa digiri 40% na rana, wanda yasa al'umma dewa na jikkata.
Da muka tun tubi wani babban jami'in wutar lantar ki na jaha wanda bai son bayyana sunan sa ba, yace, "Wasu manyan tirasfomomi ne suka lalace akan hanyar Biu zuwa maiduguri, kuma yace, "injinonin su suna kan gyarawa dan haka al'umma suci gaba da hakuri.
Sunday, 28 February 2016
SHIGA NAN DAN KA BADA SHAWARA.
Modu Sheriff Ne Yake Daukar Nauyin Boko Haram - Inji Kayode
Rikici tsakanin Sabon Shugaban Jam’iyar PDPda tsohon Ministan tsohon shugaban kasa Jonathan, Fani Kayode ya barke inda suka sa juna a gaba domin tona asirin juna.A inda Kayode ya kira Ali Modu Sheriff “Mai daukar nauyin Boko Haram” Ali Modu Sheriff ya maida martani yace masa “da abinda kake fada gaskiyane da Buhari ya kamani tuntuni”.A halin da ake ciki yanzu dai Ali Modu sheriff ya shigar da kara Kotu ta dalilin zargin da Kayode yake masa akan ya biya shi naira Biliyan 10 sannan kuma ya bukaci ya fito duniya ya bashi hakuri, sannan ya tabbatarwa da duniya cewar, "sai yayi maganin Fani Kayode".Mudai fatan mu shine Allah ya kara tona asirinazzalumai a kasar nan.
Saturday, 27 February 2016
BUHARI NA SHIRIN MAYAR DA KASAR NAN TA ISLAMA-FAYOSE
Buhari Na Shirye-shiryen Mayar Da
Nijeriya Kasar Islama, Inji Gwamna
Fayose
*Ya Kuma Ce PDP Za Ta Dawo A
2019
Daga Sani Musa, Abuja
Gwanan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya
yi zargin cewa shugaba Muhammadu
Buhari yana kule-kulen mayar da
Nijeriya kasar islama.
Ayodele Fayose ya yi wannan zargin
ne a garin Fatakwal babban birnin
jihar Ribas, wajen bikin adu'ar
godewa Allah dangane da nasara da
takwaran sa na jihar Ribas Nyesom
Wike ya yi a kotun koli.
Gwamnan wanda ya bayyana kansa a
matsayin mai ki fadi wanda ya ce
babu wanda ya isa ya taba shi, ya
shedawa jama'ar da suka halarci
taron adu'ar cewa yana wani sirri da
zai bayyana masu, inda ya yi tambayr
su ko suna son jin wannan sirrin
dangane da Shugaban kasa
Muhammadu Buhari da kuma
gwanatinsa da APC?
Sai Gwamna Fayose yace "suna nan
suna shirye-shirye mayar da kasar
nan mai bin tafarkin addinin Islama
kuma hakar su ba za ta cimma ruwa
ba, kamar yadda ba su samu nasarar
yin hakan ba a shekara ta 1984."
Gwamnan ya ce idan babu lauje cikin
ladi, menene ya sa mutum biyar suka
tafi kasar Saudiya suka jira shugaban
kasar a can idan ba su da wata
manufa?
Ya ce sannu a hankali Allah na tona
asirin su, ya ce Nijeriya kasa ce mai
tsarin addinai barkatai kuma babu
wanda ya isa ya hana wani yin
Kiristanci kuma Musulmai su yi nasu.
Gwamnan ya ce babu ko tantama
PDP za ta dawo mulkin kasar nan a
shekara ta 2019.
Subscribe to:
Comments (Atom)