Saturday, 27 February 2016

BUHARI NA SHIRIN MAYAR DA KASAR NAN TA ISLAMA-FAYOSE

Buhari Na Shirye-shiryen Mayar Da Nijeriya Kasar Islama, Inji Gwamna Fayose *Ya Kuma Ce PDP Za Ta Dawo A 2019 Daga Sani Musa, Abuja Gwanan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya yi zargin cewa shugaba Muhammadu Buhari yana kule-kulen mayar da Nijeriya kasar islama. Ayodele Fayose ya yi wannan zargin ne a garin Fatakwal babban birnin jihar Ribas, wajen bikin adu'ar godewa Allah dangane da nasara da takwaran sa na jihar Ribas Nyesom Wike ya yi a kotun koli. Gwamnan wanda ya bayyana kansa a matsayin mai ki fadi wanda ya ce babu wanda ya isa ya taba shi, ya shedawa jama'ar da suka halarci taron adu'ar cewa yana wani sirri da zai bayyana masu, inda ya yi tambayr su ko suna son jin wannan sirrin dangane da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwanatinsa da APC? Sai Gwamna Fayose yace "suna nan suna shirye-shirye mayar da kasar nan mai bin tafarkin addinin Islama kuma hakar su ba za ta cimma ruwa ba, kamar yadda ba su samu nasarar yin hakan ba a shekara ta 1984." Gwamnan ya ce idan babu lauje cikin ladi, menene ya sa mutum biyar suka tafi kasar Saudiya suka jira shugaban kasar a can idan ba su da wata manufa? Ya ce sannu a hankali Allah na tona asirin su, ya ce Nijeriya kasa ce mai tsarin addinai barkatai kuma babu wanda ya isa ya hana wani yin Kiristanci kuma Musulmai su yi nasu. Gwamnan ya ce babu ko tantama PDP za ta dawo mulkin kasar nan a shekara ta 2019.

No comments:

Post a Comment