Saturday, 27 February 2016

BANYI WA KOWA ALKAWARIN DUBU BIYAR BA-BUHARI

Ban yiwa kowa alkawalin naira dubu biyar ba, inji Buhari a Saudiyya. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewar ba inda yace zai baiwa matasa kyauta naira dubu biyar duk wata a lokacin kamfen dinsa. A jawabin da ya yiwa yan Najeriya Mazauna Saudiyya yace zancen baiwa matasa marasa aiki na naira dubu biyar zance ne a cikin manufofin kamfe na jam'iyyar APC ba na Muhammadu Buhari a matsayin dan takara ba. Haka ma ya roki yan Najeriya dake kasar Saudiyya dasu taimakawa kasarsu da addu'oi don kuwa matsalolin da kasar take fuskanta ba zai iya kawo kashe ba, sai da addua.

No comments:

Post a Comment