Saturday, 27 February 2016

WATA DODONNIYA TA BULLA A GASHIWA TANA SHA JINI

Hatsabibiyar Dodanniya Ta Bulla Da Shan Jini A Gashua — Muhammad Maitela Wasu bayanai da LEADERSHIP Hausa ta samu daga jama’a da dama a Unguwanni daban-daban da ke garin Gashuwa ta jihar Yobe, sun nuna cewa jama’a suna ci gaba da fargaba dangane da yadda wata halitta mai kama da Dodanniya ke shiga gidajen jama’a tana yin awon gaba da dabbobinsu, wanda daga bisani sai a tarar an kwashe kayan cikin dabbar an bar gangar jikin, a wani lokaci kuma sai a tarar da dabbar kwance an tsotse jininta. Bayanan suka nuna cewa, wannan babban abin al’ajabi yana ci gaba da daure wa jama’a da dama kai, bisa yadda matsalar ke ci gaba da yi masu barazanar da ta kai wasu ba sa samun runtsawa, yayin da wasu ke sintiri don tsaron unguwannin nasu har gari ya waye. Wani mazaunin wannan wuri, Malam Muhammed Abbas (Malam Awan) ya bayyana cewa, “hakika wannan al’amarin ya daure mana kai. Saboda ranar Jumu’ar da ta gabata, wannan Dodanniyar ta shiga gidan makwabcina ta kama tunkiya, inda ta kwashe kayan cikinta, ta bar gangar jikin a kofar gida. Kashe gari kuma ya sake dawowa, to shi ne sai muka fahimci abin ba na zama ba ne, sai muka fara tunanin kada fa wannan abin ya tsallaka zuwa ga ‘ya’yanmu.” Ya ci gaba da cewa, “hakan ta sa muka yi shawarar cewa ba mu ga ta zama ba,inda muka nemi matasan Unguwa majiya karfi muka rarraba su kashi-kashi a cikin Unguwar, wasu a kan itace, kuma kowanne rike da sanduna da fitilar hannu; can cikin salasainin dare sai muka gansu sun tunkaro mu su biyu, shi ne daya daga cikinmu ya dalla masu hasken fitila, cikin tsoro sai suka fita a guje, muka bi su,mutane sun tasamma dari, daya daga cikin Dodannin, wajen shan kwana sai da ya yi karo da katanga, kamar ya fadi, a haka ya shanye kwanar. Kuma abin mamaki, hatta karnuka da suka gansu, fadawa cikin gida suka yi, kuma kafafunsu hudu ne kamar dangin kura, kuma kamar mutum daga gaba, sannan babu jela, amma da muka rutsa shi sai ya bata bat.” Malamin ya kara da bayyana cewa,suna cikin matukar fargabar wannan al’amarin, inda ya ce, “kasancewar yadda wannan abu ke mana ta’adi, musamman yadda ba ya kama ramammen rago ko tinkiya, sai kosasshe, kuma ba ya cin akuya, yanzu haka wasu sun sayar da dabbobin su. Sannan yanzu mun yi shawarar mu hadu mu gaya wa Sarkin Bade halin da ake ciki. Sannan za mu shaida wa jami’an tsaron ’yan sanda da sojoji don gudun kada matsalar ta wuce inda take yanzu. Amma gaskiya muna fuskantar damuwa.” Ita kuma Malama Jimmala, wacce wannan abu ya sungume mata tinkiya, sannan ya wawushe kayan cikinta ya jefar da ita a kofar gida, ta bayyana cewa, “da misalin karfe biyu muna daki sai muka ji motsi a waje, dayake mun dan tsorata, ba mu fito ba, shiru har gari ya waye, shi ne sai muka ga babu tinkiyarmu, mun dauka ko barawo ne, abin mamaki sai muka ganta a kofar gida a mace bayan an kwashe kayan cikinta. Sannan wani abin mamaki, babu wata alamar jini ya zuba.” Bisa ga bayanan da wakilinmu ya tattaro a garin, sun bayyana cewa wannan Dodo ya karade Unguwanni da dama, tare da hallaka dabbobi masu yawa, sannan kuma duk wani abu da jama’a ke yi ta hanyar yi masa a-tare, abin ya faskara. Saboda wani lokaci sai an yi masa kofar rago, amma sai ya sulale a rasa inda ya shiga. Amma dai wasu da suka sha yin arangama da ita sun ce, wani lokaci ta kan zo a siffar mutum, wani zubin kuma kamar kura, amma babu jela.

No comments:

Post a Comment