Saturday, 27 February 2016
YAN BOKO-HARAM KUSAN 30, SUKA MIKA WUYA.
Rahotanni daga Damboa dake jihar borno na cewa، "Akalla yan Boko-Haram 30, ne suka mika wuya ga sojojin nigeria inda sun ce,"sun gaji da yaki ne kuma basu da yanda zasuyi shine sun mika wuya, dan gwamnatin nigeria tayi musu afwa.
Haka lamarin yake a SABONGARI dake karamar hukumar Damboa inda su kuma yan Boko-Haram guda biyu 2 ne sun mika makaman su ga sojoji.
Sai dai a gefe guda kuma al'ummar yankin suna kira ga sojoji kada su karbi afuwan yan ta'adda a cewar su a kashe su kawai.
Sai dai masu sharhi na cewa, "in da gaske ne suka sallama a karbe su sannan a samu wani guri a juye musu wannan muguwar akida sannan daga baya gwamnati ta samar musu da aikin yi, suka ce idan har an kashe su idan wasu suna da niyyar yin haka to bazasuyi ba zasu gwammace su mutu.
A NAKU TUNANIN YA GWAMNATI ZATAYI DA WADAN DA SUKA MIKA WUYA
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment