Saturday, 27 February 2016

El'rufa'i yayi kuskure akan dokan wa'azi-inji majalisar malamai

El Rufa'i Ya Tafka Kuskure Akan Dokokin Wa'azi Da Ya Kafa, Inji Majalisar Limamai Da Malamai Ta Jihar Kaduna DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA Majalisar Limamai da Malaman Jihar Kaduna, ta yi tir gami da Allah wadai, akan matakin da gwamnan jihar, Malam Nasiru El-Rufa'i ya dauka, na kaddamar da dokokin wa'azi a jihar. Da yake bayani gaban manema labarai a Kaduna, Shugaban Majalisar Malaman, Al Sheik Usman Baban Tune, ya ce da akwai kuskure babba da gwamnan ya yi na yin kokarin shiga sabga ta Addini, da yin katsalandan akan harkar ta Malamta, wanda wannan inji Malamin ba karamar tawayace zai haifar a cikin tsarin gwamnatinsa ba. Shugaban Majalisar Malaman ya ci gaba da cewar, sun shiga cikin wani yanayi lokacin da suka ga takardar dokokin Wa'azin wacce aka rubutata cikin harshen Turanci, kuma nan take suka sa aka fassara ta zuwa harshen Hausa, sannan aka rarraba ta ga Malamai da Limamai dake Jihar domin kara fahimtar Takardar, sannan suka yi shiri na musanman zuwa Majalisar Dokokin jihar inda suka gana da Shugaban Majalisar dokokin da sauran Wakilan Majalisar akan lamarin, kuma bisa ga dukkan alamu 'Yan Majalisun dokokin suna da fahimta da tarbiyar addini, domin sun tabbatar musu ba za su amince da wannan doka ba har sai idan sun yi zama da Malamai. Sheik Baban Tune, ya kara da cewar, gwamnati ta Musulunci dake taimakawa Musulunci, ita ce take da damar tsarawa Malamai yadda za su gudanar da Wa'azi, ba Gwamnatin da ta yi hannun riga da Musulunci ba, babu wani tagomashin da Musulunci ko Malaman Musulunci suke samu daga gareta. Malamin ya bayyana cewa, dukkanin Malaman Musulunci da na Kiristanci a Jihar, sun yi tarayya wajen la'antar wannan kuduri na gwamnan, domin babu alama na fahimta a ciki, saboda a cikin takardar dokokin an bayyana cewar, za a kafa wata hukuma wacce JNI da CAN za su kasance a karkashinta, sannan wannan hukuma za ta sanya ido akan harkar wa'azi, karkashin mai baiwa gwamna shawara akan harkar tsaro, da wakilcin 'yan sanda, da bangaren Shari'a, inda ya ce wannan kadai ya isa ya nuna rashin adalci.

No comments:

Post a Comment