Wednesday, 29 June 2016

AN SHAFE SAMA DA WATA UKU BABU WUTAR LANTAR KI A BORNO

AN SHAFE WATA UKU BABU HASKEN WUTAR LANTARKI A BORNO. Daga wakilin mu BIN ISMAIL ALI MAIDUGURI. Yau kimanin wata uku kenan babu hasken wutar lantarki a jihar borno, wanda haka yasa jama'a cikin kakani kayi inda, wanda har takai mai martaba shehun BORNO kira akan ayi gaggawa a samarwa jahar wutar lantarki, dan su samu susha ruwa mai sanyi a wannan wata mai albarka, amma gashi mun doshi karewan wannan wata na Ramadan amma har yanzu babu alamar wuta a jihar wanda har takai wasu na cewa, "kodai mun sallamo wutar ne baki daya. Wakilin mu ya zaka dan ganewa idanun sa yanda mutane suke rayuwa tun bayan daukewar wutar lantarki, jama'a dewa sun bayyana cewa, "abun yazo musu ne ba zata inda da wasa -wasa har yanzu mun shafe wata uku. Shi kuma assale MUHAMMAD Tahir cewa yayi, "muna cikin matsanan cin wahala na samun ruwan sha musamman a wannan wata mai albarka, inda ya kara da cewa, "in kaga wuta to sai wanda yake da hali wato yana da injin bada wutar. Sai dai duk kokarin da wakilin mu yayi na jin ta bakin jami'an wutar lantarki ya ci tura inda ya ziyarci ofishin su bai samu kowa ba.

TARIHIN T.Y BURATAI.

TARIHIN TUKUR YUSUF BURUTAI. . Lieutenant General Yusif Tukur Buratai: . Sunansa Tukur Yusuf Buratai, amma ana kiransa da ‘T.Y Buratai’. An haife shi a garin Buratai dake karamar hukumar Biu ta jihar Borno, a ranar 24 ga watan Nuwamba a shekarar 1960. Don haka, Buratai ɗan asalin jihar Borno ne dake arewa maso gabashin Najeriya. ↓ Laftana Janar TY Buratai shi ne hafsan Sojoji na 26 a tarayyar Najeriya, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya naɗa a ranar 13 ga watan Juni na shekarar 2015. ↓ Buratai ya yi karatun Furamari a garinsu buratai, daga nan ya zarce zuwa Kwalejin Malaman Gwamnati dake garin Potiskum a jihar Yobe. A watan Junairu na shekarar 1981, Buratai ya halarci Nigerian Defence Academy dake Kaduna a matsayin ɗaya daga cikin membobi a shirin nan na ‘29 Regular Combatant Course (29R)’. Haka zalika, Buratai ya samu takardar shaidar kammala Jami’a, wato Digiri a fannin History daga Jami’ar Maiduguri. Kuma yana da Digiri a fannin Philosophy daga Jami’ar Bangladesh University of Professions dake garin Dhaka. ↓ Kafin naɗinsa a matsayin hafsan Soji, Buratai shi ke jagorantar rundunar tsaro ta hadin–gwiwa wacce ke da hedikwata a birnin Ndjamena na kasar Chadi. Kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da kuma Benin ne suka kafa rundunar domin yaki da ’yan ta’addan da ke yankinsu. ↓ A baya dai, Janar Buratai ya yi aiki a matsayin Kwamandan runduna ta Biyu ta sojin Najeriya dake birnin Fatakwal na jihar Rivers, sannan ya taba zama Kwamandan makarantar horas da sojin kasa dake Jaji, a jihar Kaduna. ↓ TY Buratai ya samu ci gaba ainun wajen aikinsa da kuma karin girma kamar haka: • Lieutenant (January 1985) • Captain (January 1989) • Major (January 1994) • Lieutenant Colonel (January 1998) • Colonel (January 2004) • Brigadier General (January 2009) • Major General (January 2012) • Lieutenant General (August 2015) ↓ TY Buratai ya samu kambi da lambobin yabo a wurare daban–daban da suka haɗa da: • Forces Service Star (FSS) • Meritorious Service Star (MSS) • Distinguished Service Star (DSS) • Grand Service Star (GSS). • Pass Staff Course Dagger (PSCD) • Field Command Medal • Training Support Medal • United Nations Medal for Angolan Verification Medal II 26-12-2015 Allah ya karawa rayuwar ka albarka T.Y burutai, ya baka ikon yin daidai, ya kare ka daga dukkan sharri, ya kuma hadaka da dukkan alkhairi. Amin.

Tuesday, 28 June 2016

KOTU TA BADA UMARNIN GARKAME KAYODE

Kotu Ta Bada Umarnin Garkame Fani Kayode, Nenadi Usman Wata kotun tarayya ta bada umarnin garkame tsohon Ministan Sufurin jiragen sama, Fani Kayode da takwararsa na ma'aikatar kudi, Nenadi Usman bisa zargin almundahanar Naira Bilyan 1,5. Mai Shari'a kotun, Suleman Hassan ya ki bada belinsu ne bayan da lauyan EFCC ya nemi a bashi lokaci don yin nazari kan bukatar wadanda ake tuhumar na neman beli. Kudaden dai na daga cikin kudaden makamai wadanda aka yi amfani da su a lokacin yakin zaben Jonathan wanda Fani Kayode ne mai Magana da yawun kungiyar yakin neman zaben.

Sunday, 12 June 2016

JIHAR BORNO TA SHAFE SAMA DA WATA DAYA BABU WUTAR LANTAR KI.

Al-ummar jihar borno sun shafe sama da wata daya, basu da wutar lantar ki, kuma suna cikin matsanan cin wahala saboda yanayin zafin da suke ciki kuma basa samun ruwan sha mai sanyi, yanda ya kamata, kwamakin baya mai martaba shehun borno Umar Garbai el-amin elkanami, yayi kira da a gaggauta kawo wuta dan al'umma ta samu sa'idar rayuwa, amma har yanzu suna fiskan tar wannan matsala, inda zafin rana yana kai wa digiri 40% na rana, wanda yasa al'umma dewa na jikkata. Da muka tun tubi wani babban jami'in wutar lantar ki na jaha wanda bai son bayyana sunan sa ba, yace, "Wasu manyan tirasfomomi ne suka lalace akan hanyar Biu zuwa maiduguri, kuma yace, "injinonin su suna kan gyarawa dan haka al'umma suci gaba da hakuri.

Sunday, 28 February 2016

SHIGA NAN DAN KA BADA SHAWARA.


MUNA BUKATAR KU BAIYA NA MANA RA'AYIN KU DAN GANE DA YANDA MUKE WATSO MUKU SHIRYE SHIRYEN MU, ZAKU IYA BAIYANA A NAN KASA DON MU SAMU KARFIN GWIWAR AIKA MUNA GODIYA BAIYA NA RA'AYIN KA YANZU.

Modu Sheriff Ne Yake Daukar Nauyin Boko Haram - Inji Kayode

Rikici tsakanin Sabon Shugaban Jam’iyar PDPda tsohon Ministan tsohon shugaban kasa Jonathan, Fani Kayode ya barke inda suka sa juna a gaba domin tona asirin juna.A inda Kayode ya kira Ali Modu Sheriff “Mai daukar nauyin Boko Haram” Ali Modu Sheriff ya maida martani yace masa “da abinda kake fada gaskiyane da Buhari ya kamani tuntuni”.A halin da ake ciki yanzu dai Ali Modu sheriff ya shigar da kara Kotu ta dalilin zargin da Kayode yake masa akan ya biya shi naira Biliyan 10 sannan kuma ya bukaci ya fito duniya ya bashi hakuri, sannan ya tabbatarwa da duniya cewar, "sai yayi maganin Fani Kayode".Mudai fatan mu shine Allah ya kara tona asirinazzalumai a kasar nan.

Saturday, 27 February 2016

BUHARI NA SHIRIN MAYAR DA KASAR NAN TA ISLAMA-FAYOSE

Buhari Na Shirye-shiryen Mayar Da Nijeriya Kasar Islama, Inji Gwamna Fayose *Ya Kuma Ce PDP Za Ta Dawo A 2019 Daga Sani Musa, Abuja Gwanan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya yi zargin cewa shugaba Muhammadu Buhari yana kule-kulen mayar da Nijeriya kasar islama. Ayodele Fayose ya yi wannan zargin ne a garin Fatakwal babban birnin jihar Ribas, wajen bikin adu'ar godewa Allah dangane da nasara da takwaran sa na jihar Ribas Nyesom Wike ya yi a kotun koli. Gwamnan wanda ya bayyana kansa a matsayin mai ki fadi wanda ya ce babu wanda ya isa ya taba shi, ya shedawa jama'ar da suka halarci taron adu'ar cewa yana wani sirri da zai bayyana masu, inda ya yi tambayr su ko suna son jin wannan sirrin dangane da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwanatinsa da APC? Sai Gwamna Fayose yace "suna nan suna shirye-shirye mayar da kasar nan mai bin tafarkin addinin Islama kuma hakar su ba za ta cimma ruwa ba, kamar yadda ba su samu nasarar yin hakan ba a shekara ta 1984." Gwamnan ya ce idan babu lauje cikin ladi, menene ya sa mutum biyar suka tafi kasar Saudiya suka jira shugaban kasar a can idan ba su da wata manufa? Ya ce sannu a hankali Allah na tona asirin su, ya ce Nijeriya kasa ce mai tsarin addinai barkatai kuma babu wanda ya isa ya hana wani yin Kiristanci kuma Musulmai su yi nasu. Gwamnan ya ce babu ko tantama PDP za ta dawo mulkin kasar nan a shekara ta 2019.

BANYI WA KOWA ALKAWARIN DUBU BIYAR BA-BUHARI

Ban yiwa kowa alkawalin naira dubu biyar ba, inji Buhari a Saudiyya. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewar ba inda yace zai baiwa matasa kyauta naira dubu biyar duk wata a lokacin kamfen dinsa. A jawabin da ya yiwa yan Najeriya Mazauna Saudiyya yace zancen baiwa matasa marasa aiki na naira dubu biyar zance ne a cikin manufofin kamfe na jam'iyyar APC ba na Muhammadu Buhari a matsayin dan takara ba. Haka ma ya roki yan Najeriya dake kasar Saudiyya dasu taimakawa kasarsu da addu'oi don kuwa matsalolin da kasar take fuskanta ba zai iya kawo kashe ba, sai da addua.

LABARU DA DUMI DUMI WANI BOM YA TASHI A KAMARUN

Rahotanni daga garin BANGUR da ke Lardin Arewa mai Nisa Sun tabbatar da cewa Wani BOMB ya tashi a garin. Wanda hakan yayi Sanadiyyar mutuwar Wasu Sojoji. Har ma Ana cewa Lamarin ya ritsa da dagacin garin.

WATA DODONNIYA TA BULLA A GASHIWA TANA SHA JINI

Hatsabibiyar Dodanniya Ta Bulla Da Shan Jini A Gashua — Muhammad Maitela Wasu bayanai da LEADERSHIP Hausa ta samu daga jama’a da dama a Unguwanni daban-daban da ke garin Gashuwa ta jihar Yobe, sun nuna cewa jama’a suna ci gaba da fargaba dangane da yadda wata halitta mai kama da Dodanniya ke shiga gidajen jama’a tana yin awon gaba da dabbobinsu, wanda daga bisani sai a tarar an kwashe kayan cikin dabbar an bar gangar jikin, a wani lokaci kuma sai a tarar da dabbar kwance an tsotse jininta. Bayanan suka nuna cewa, wannan babban abin al’ajabi yana ci gaba da daure wa jama’a da dama kai, bisa yadda matsalar ke ci gaba da yi masu barazanar da ta kai wasu ba sa samun runtsawa, yayin da wasu ke sintiri don tsaron unguwannin nasu har gari ya waye. Wani mazaunin wannan wuri, Malam Muhammed Abbas (Malam Awan) ya bayyana cewa, “hakika wannan al’amarin ya daure mana kai. Saboda ranar Jumu’ar da ta gabata, wannan Dodanniyar ta shiga gidan makwabcina ta kama tunkiya, inda ta kwashe kayan cikinta, ta bar gangar jikin a kofar gida. Kashe gari kuma ya sake dawowa, to shi ne sai muka fahimci abin ba na zama ba ne, sai muka fara tunanin kada fa wannan abin ya tsallaka zuwa ga ‘ya’yanmu.” Ya ci gaba da cewa, “hakan ta sa muka yi shawarar cewa ba mu ga ta zama ba,inda muka nemi matasan Unguwa majiya karfi muka rarraba su kashi-kashi a cikin Unguwar, wasu a kan itace, kuma kowanne rike da sanduna da fitilar hannu; can cikin salasainin dare sai muka gansu sun tunkaro mu su biyu, shi ne daya daga cikinmu ya dalla masu hasken fitila, cikin tsoro sai suka fita a guje, muka bi su,mutane sun tasamma dari, daya daga cikin Dodannin, wajen shan kwana sai da ya yi karo da katanga, kamar ya fadi, a haka ya shanye kwanar. Kuma abin mamaki, hatta karnuka da suka gansu, fadawa cikin gida suka yi, kuma kafafunsu hudu ne kamar dangin kura, kuma kamar mutum daga gaba, sannan babu jela, amma da muka rutsa shi sai ya bata bat.” Malamin ya kara da bayyana cewa,suna cikin matukar fargabar wannan al’amarin, inda ya ce, “kasancewar yadda wannan abu ke mana ta’adi, musamman yadda ba ya kama ramammen rago ko tinkiya, sai kosasshe, kuma ba ya cin akuya, yanzu haka wasu sun sayar da dabbobin su. Sannan yanzu mun yi shawarar mu hadu mu gaya wa Sarkin Bade halin da ake ciki. Sannan za mu shaida wa jami’an tsaron ’yan sanda da sojoji don gudun kada matsalar ta wuce inda take yanzu. Amma gaskiya muna fuskantar damuwa.” Ita kuma Malama Jimmala, wacce wannan abu ya sungume mata tinkiya, sannan ya wawushe kayan cikinta ya jefar da ita a kofar gida, ta bayyana cewa, “da misalin karfe biyu muna daki sai muka ji motsi a waje, dayake mun dan tsorata, ba mu fito ba, shiru har gari ya waye, shi ne sai muka ga babu tinkiyarmu, mun dauka ko barawo ne, abin mamaki sai muka ganta a kofar gida a mace bayan an kwashe kayan cikinta. Sannan wani abin mamaki, babu wata alamar jini ya zuba.” Bisa ga bayanan da wakilinmu ya tattaro a garin, sun bayyana cewa wannan Dodo ya karade Unguwanni da dama, tare da hallaka dabbobi masu yawa, sannan kuma duk wani abu da jama’a ke yi ta hanyar yi masa a-tare, abin ya faskara. Saboda wani lokaci sai an yi masa kofar rago, amma sai ya sulale a rasa inda ya shiga. Amma dai wasu da suka sha yin arangama da ita sun ce, wani lokaci ta kan zo a siffar mutum, wani zubin kuma kamar kura, amma babu jela.

SARAKI YA SIRKA TSIYA, YA KASHE MILYON 300,

Saraki Ya Sayi Motocin Alfarma Na Milyoyin Kudade Duk Da Fama Da Matsalar Tattalin Arzikin Kasa Da Ake Yi Duk da matsanancin rashin kudi da tattalin da Gwamnatin Tarayya ta ke yi wajen tanada kudaden kasa domin yin ayyukan ci gaban kasa, shugaban majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki ya canza motocin hawansa, inda zuwa yanzu dai guda hudu ne suka riga suka zo, kuma har ya fara amfani da su. Rahotanni sun nuna cewa an kashe sama da Naira Miliyan 300 wajen siyansu. Sauran guda shidan da suka rage suna kan hanya. Cikin motocin da suke kasa yanzu sun hada da mota kirar Marsandi (2016) akan Naira Miliyan 49 ko wace daya da mota kirar Toyota (2016) akan kudi sama da Naira Miliyan 100. Majiya: Premium Times

El'rufa'i yayi kuskure akan dokan wa'azi-inji majalisar malamai

El Rufa'i Ya Tafka Kuskure Akan Dokokin Wa'azi Da Ya Kafa, Inji Majalisar Limamai Da Malamai Ta Jihar Kaduna DAGA IBRAHIM AMMANI, KADUNA Majalisar Limamai da Malaman Jihar Kaduna, ta yi tir gami da Allah wadai, akan matakin da gwamnan jihar, Malam Nasiru El-Rufa'i ya dauka, na kaddamar da dokokin wa'azi a jihar. Da yake bayani gaban manema labarai a Kaduna, Shugaban Majalisar Malaman, Al Sheik Usman Baban Tune, ya ce da akwai kuskure babba da gwamnan ya yi na yin kokarin shiga sabga ta Addini, da yin katsalandan akan harkar ta Malamta, wanda wannan inji Malamin ba karamar tawayace zai haifar a cikin tsarin gwamnatinsa ba. Shugaban Majalisar Malaman ya ci gaba da cewar, sun shiga cikin wani yanayi lokacin da suka ga takardar dokokin Wa'azin wacce aka rubutata cikin harshen Turanci, kuma nan take suka sa aka fassara ta zuwa harshen Hausa, sannan aka rarraba ta ga Malamai da Limamai dake Jihar domin kara fahimtar Takardar, sannan suka yi shiri na musanman zuwa Majalisar Dokokin jihar inda suka gana da Shugaban Majalisar dokokin da sauran Wakilan Majalisar akan lamarin, kuma bisa ga dukkan alamu 'Yan Majalisun dokokin suna da fahimta da tarbiyar addini, domin sun tabbatar musu ba za su amince da wannan doka ba har sai idan sun yi zama da Malamai. Sheik Baban Tune, ya kara da cewar, gwamnati ta Musulunci dake taimakawa Musulunci, ita ce take da damar tsarawa Malamai yadda za su gudanar da Wa'azi, ba Gwamnatin da ta yi hannun riga da Musulunci ba, babu wani tagomashin da Musulunci ko Malaman Musulunci suke samu daga gareta. Malamin ya bayyana cewa, dukkanin Malaman Musulunci da na Kiristanci a Jihar, sun yi tarayya wajen la'antar wannan kuduri na gwamnan, domin babu alama na fahimta a ciki, saboda a cikin takardar dokokin an bayyana cewar, za a kafa wata hukuma wacce JNI da CAN za su kasance a karkashinta, sannan wannan hukuma za ta sanya ido akan harkar wa'azi, karkashin mai baiwa gwamna shawara akan harkar tsaro, da wakilcin 'yan sanda, da bangaren Shari'a, inda ya ce wannan kadai ya isa ya nuna rashin adalci.

YAN BOKO-HARAM KUSAN 30, SUKA MIKA WUYA.

Rahotanni daga Damboa dake jihar borno na cewa، "Akalla yan Boko-Haram 30, ne suka mika wuya ga sojojin nigeria inda sun ce,"sun gaji da yaki ne kuma basu da yanda zasuyi shine sun mika wuya, dan gwamnatin nigeria tayi musu afwa. Haka lamarin yake a SABONGARI dake karamar hukumar Damboa inda su kuma yan Boko-Haram guda biyu 2 ne sun mika makaman su ga sojoji. Sai dai a gefe guda kuma al'ummar yankin suna kira ga sojoji kada su karbi afuwan yan ta'adda a cewar su a kashe su kawai. Sai dai masu sharhi na cewa, "in da gaske ne suka sallama a karbe su sannan a samu wani guri a juye musu wannan muguwar akida sannan daga baya gwamnati ta samar musu da aikin yi, suka ce idan har an kashe su idan wasu suna da niyyar yin haka to bazasuyi ba zasu gwammace su mutu. A NAKU TUNANIN YA GWAMNATI ZATAYI DA WADAN DA SUKA MIKA WUYA

KUNA IYA AIKO MANA DA LABARU TA EMAIL.

KUNA IYA AIKO MANA DA LABARU TA ADRESHIN MU NA EMAIL A BORNOHAUSA@GMAIL.COM SAI KUCI GABA DA AIKO MANA LABARU DA YANA YIN WAJA JEN KU. MUNGODE.

BAZAMU HANA YANCIN MAGANA BA-SARAKI

Ba Za Mu Samar Da Dokar 'Yancin
Fadin Albarkacin Baki Ba A Kafafen
Sadarwa, Inji Shugaban Majalisar
Dattijai, Sanata Bukola Sadaki

GEN.BURATAI YA BUDE HANYAR DAMBOA

A safiyar yau ne shugaban rundunar sojoji gen buratai ya bude hanyar da ta tashi daga maiduguri zuwa Damboa, gen buratai shine ya jagoran ci bude hanya, inda masu gani da ido suka ce, "Sunga al'ummar Damboa wadan da rikicin Boko Haram ya tilas ta musu fita daga cikin gari Damboa suna ta murna tare da jin jinawa shugaban sojojin buratai.

Haka lamarin yake a can karamar hukumar Damboa jama'a da dama ne suka fito akan titi dan tarbar ayarin sojoji da kuma wasu jama'a da suka bi tawagar.

SHEKARA HUDU AN GAGARA GYARA GADA.

SHEKARA HUDU AN GAGARA GYARA GADA.
.
GA CIKEKKEN RAHOTAN ZIYARAR DA BORNO HAUSA NEWS TA KAI CIKIN GARIN MAIDUGURI.
.
A bayan munyi ziyara a cikin maiduguri babban birnin jihar borno muna cikin tafiya sai muka yi cikibis da wani GADA da ake gyarawa, sai muka sauka muka tambayi mazauna unguwa inda muka ce me sunan wannan unguwa sai suka ce sunan ta Lagos sitirid.
Da muka tambaye su yaushe aka fara wannan GADA da ake yi a unguwar ku? sai suka kada baki suka ce," wannan GADAR yau kusan shekara hudu kenan, har yanzu ba'a gama kammalawa ba, malam baana, yace sun cika unguwar mu da K'URA kuma sun hana al'umma bi ta wannan hanya amma har yau sun gagara gyarawa inji BAANA.
Munci gaba da ziyara a cikin gari ko zamu yi cikibis da wani aiki na azo a gani a cikin maiduguri amma idan mu bai kai gurin ba, har mun bar welcome to na fita zuwa bama amma idan mu bai bamu wani abu sabo ba a cikin maiduguri, hatta manyan titinu na cikin gari idan kana bi zaka iske wasu wurare da suke da ramuka har sai ka dau kan mota a wasu wurare, sai dai wani mai suna BAKURA, magoyi bayan gwamna ne kuma dan jam'iyyar APC yace, "Ai gwamna yana kokari matuka inda ya buga misali da yan gudun hijra yace, ana kula dasu sosai ana basu abunci da ruwan sha da sauran buka tu na yau da kullum dan haka gwamnatin jihar borno tana aiki tukuru, da muka tambaye shi akan cewa, "al'umma suna kokawa wai ba'a gyara musu hanya basu ganin abubuwan more rayuwa ba, sai ya kada baki yace, "ina gwamna ya samu hankalin sa masu fadin haka suyi hakuri anyi kusa gama da yan Boko Haram in an gama dasu zasu ga canji da abubuwa dewa.
.
Sai dai a bangare guda kuma al'umman dake zaune a maiduguri sun musan ta wannan magana inda suka ce, "sam wannan ba dalili ba, gwamna ya labe da batun tsaro yana wawushe kudin jahar su baya musu aiki sannan yan gudun hijra basa samun wata tallafin azo a gani a cikin jihar inda a halin yanzu yan gudun hijra suna gara ramba a cikin gari suna neman abun sawa a bakin salati -inji GARBA DA BAKWOLO.
.
Daga nan sai muka wuce i zuwa san sanin yan gudun hijra wanda yake a kan hanyar da ta fita i zuwa BAMA , a kwai mu dauke da rahoto a nan gaba.

BUHARI YA NUFI QATAR

A yau Jirgin Shugaba
Muhammadu Buhari Zai Nufi Kasar
Qatar Bayan Kammala Ziyarar Aiki Da
Ibada A Kasar Saudi Arabia.
Shugaba Buhari da shugaban Qatar
da sauran kasashen da ke da man
fetur a duniya, za su tattauna ne kan
matsalar karyewar farashin mai a
kasuwannin duniya

AN SOMA YIN SHINKAFA A NIGERIA

Dokokin Buhari Ya Sanya Wasu 'Yan
Kasuwa Soma Raya Masana'antun
Cikin Gida
Kafewar da shugaba Muhammadu
Buhari ya yi na cewa ba zai karya
darajar naira ba ya sanya wasu daga
cikin masu shigo da shinkafa
dawowa gidan don kafa kamfanonin
casar shinkafa a gidan don samar da
shinkafa nagartacciya ga al'ummar
Nijeriya kan farashi mai sauki.
Kwanakin baya ma an sanu wabi
kamfanin shinkafa a jihar Jigawa. A
yau kuma sai ga wata sabuwar
shinkafar gwamnati 'yar jihar Kano.
Wadda gonar "Umza international
farms Ltd" dake kan 13km idan ka
saki hanyar Zaria kafin kwanar
dawaki Kano.
Tuni wasu suka soma nazarin cewa
hakika Buhari ya shirya don samar da
abinci mai sauki ga talaka. Kuma
hakan zai samar da ayyukan yi da
kuma saukin rayuwa a kasa. Wanda
hakan ya sa suke kira ga cewa ya
zama wajibi a baiwa shugaban goyon
baya wajen daina siyan kayan

kasashen waje, muddin ga na gida.

BORNO HAUSA TA SAMU CI GABA

ASSALAMU ALAIKUM WANNAN SHAFI KARI NE DA KUMA CI GABA DA WANNAN KAFA TA BORNO HAUSA NEWS TAKE SAMU DAN HAKA SAI KUCI GABA DA KASAN CE DAMU, KO TA EMAIL A BORNOHAUSA@GMAIL.COM KO TA FACEBOOK MUN GODE .